Labaran Kano
Majalisar ta bukaci gwamnati ta gina makarantun firamare a karamar hukumar Ungogo
Majalisar dokokin jihar Kano ta yi kira da babbar murya ga gwamnatin jihar Kano da ta gina Sababbin makarantun firamare a wasu unguwanni da garuruwa guda goma sha daya da ke yankin karamar hukumar Ungogo.
Hakan ya biyo bayan amincewa da kudrin da Dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Ungogo Aminu Sa’ad Ungogo ya gabatar yayin zaman majalisar da ya gudana a ranar lititin.
Da ya ke zantawa da manema labarai bayan kammala zaman majalisar, Aminu Sa’ad Ungogo, ya ce, sakamnakon Karin yawan jama’a a yankin ya sanya su ke da bukatar karin makarantun firamare, Wanda ya ce hakan zai taimaka wajen kaddamar da shirin ba da ilimi kyauta da gwarmnatin Kano ta kaddamar a wannan shekara.
Yankunan da ke bukatar sababbin makarantun firamare sun hada da Sharifai-kadage da Bachirawa Yamma da Tudun Rubudi da Rumawa da Zaura Kadage de Kuma Rijiyar Zaki-Arewa. Sauran sune Zangen Kaya da Karon Buzaye da Gandar da Unguwarafa da Kuma Daurawa.