Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

An bukaci Gwamnatin Kano ta gyara wasu tituna a karamar hukumar Gwarzo

Published

on

Majalisar dokokin jihar ta Kano ta bukaci gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya gyara wasu tituna guda biyu da suka lalace a yankin karamar hukumar Gwarzo.

Majalisar ta yi Wannan Kiran ne biyo bayan kudirin da dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Gwarzo Alhaji Yunusa Haruna Kayyu ya gabatar a zaman majalisar na ranar litinin.

Da yake zantawa da manema labarai bayan kammala zaman majalisar, Yunusa Haruna Kayyu, ya ce lalacewar hanyar ya janyo asara mai tarin yawa ga al’ummomin yankunan sakamakon tsaikon da ya ke kawo wejen sufiri.

Wakilin mu na majalisar dokokin jihar Kano Abdullahi Isah ya ruwaito Dan majalisar na bayyana hanyoyin wanda suka hada da hanyar ta da tashi daga Nassarawa zuwa Lakwaya mai nisan kilomita ashirin da takwas da watta ta tashi daga Gwarzo zuwa Kutama mai tsawon bakwai.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!