Labarai
Majalisar tarayya ta karyata karbar tallafin miliyan 100 daga gwamnati
Majalisar wakilai ta musanta ikirarin da shugabannin kungiyar kwadagon Najeriya suka yi na cewa gwamnatin tarayya ta baiwa ‘yan majalisar wakilai N100m a matsayin tallafi.
Shugaban kwamitin majalisar kan harkokin yada labarai da hulda da jama’a, Akin Rotimi, ya bayyana zargin a matsayin mara tushe kuma “wanda bashi da gaskiya”.
Mataimakin sakataren NLC na kasa, Christopher Onyeka ne ya yi wannan zargin a wata sanarwa da ya fitar a Abuja
Sanarwar ta kara da cewa, “Majalisar wakilai ta lura da rahotannin da ke nuna damuwa a jaridu da dama da kuma kafafen yada labarai na yanar gizo, na wata sanarwa da aka bai wa mataimakin babban sakataren kungiyar NLC, Mista Christopher Onyeka.
“Muna ganin rashin gaskiya ne kuma abin bakin ciki ne cewa Mista Onyeka zai bayyana gaskiya a wani yunkuri na neman amincewa da wasu bukatu na NLC a yayin da yake neman tozarta Majalisar Dokoki ta kasa da kuma tunzura jama’a a kan hukumar.
Tun da farko dai
Yana Mai cewa ‘mun bayyana dalla-dalla cewa Mista Onyeka ya yi karya a ikirarin da ya yi cewa an bai wa ‘yan majalisar kasa Naira miliyan 100 a matsayin kuɗin kashewa, don kaucewa shakku, babu wani lokaci da ‘yan majalisar wakilai suka samu wani kudi daga bangaren zartarwa a matsayin abin da zai taimaka musu. Don haka, muna ɗaukar wannan magana a matsayin ƙarya.
You must be logged in to post a comment Login