Labarai
Majalisar tattalin arziki : Yemi Osinbajo ya nemi jihohi su kafa kwamitin tsaro
Majalisar kula da tattalin arzikin kasa ta bukaci gwamnonin johohin kasar nan talatin da shida da su gaggauta kafa wani kwamiti na musamman kan harkokin tsaro da kuma kare hakkin bil adama, wanda zai rika sanya idanu kan ayyukan sabon sashen ‘yan sanda na musamnan da rundunar ‘yan sandan kasar nan ta kafa.
A daren jiya ne dai kwamitin ya fitar da sanarwar da ke ba da umarnin kafa kwamitin don kawo karshen cin zarafin jama’a da ake zargin ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro nayi.
Kwamitin kula da tattalin arzikin wanda mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ke jagoranta, ya kuma bukaci jihohin da su kafa wani kwamiti na musamman wanda zai rika karbar korafin jama’a wadanda suke zargin ‘yan sanda sun taba cin zarafinsu ko kashe musu ‘yan uwa .
Kwamitin na gwamnatin tarayya ya kuma bukaci al’ummar kasar nan wadanda suke zargin ‘yan sanda sun taba cin zarafinsu ko kashe musu ‘yan uwar ba bisa ka’ida ba, dasu zo gaban kwamitin na jihohi don gabatar da korafinsu,
A cewar kwamitin matukar aka binciko aka gano gaskiyar zargin da mutanen su ka yi, ba ko shakka gwamnatin za ta dauki tsauraran matakai don hukunta wadanda aka kama da laifi.
You must be logged in to post a comment Login