Connect with us

Labarai

Gwamna Abba ya taya Musulmi murnar shiga shekarar 1448

Published

on

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya taya al’ummar Musulmi na Kano da ma Najeriya baki ɗaya murnar shiga sabuwar shekarar Musulunci ta 1448 bayan Hijira.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban Daraktan yaɗa labaran Gwamnan Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar.

Ta cikin sanarwar, ya ce, gwamnan ya bayyana cewa sabuwar shekarar Musulunci wata dama ce ta yin tunani kan darussan Hijirar Annabi Muhammad (SAW), musamman game da haƙuri, sadaukarwa, jajircewa da cikakken dogaro ga Allah.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce Hijirar Annabi daga Makkah zuwa Madina ba tafiya ce kawai ba, illa wani babban sauyi da ya kafa tubalin al’umma mai adalci, tausayi da haɗin kai.

Sanarwa ta kara da cewa Gwamnan, ya yi kira ga al’ummar Musulmi da su yi amfani da wannan lokaci wajen ƙarfafa dangantakarsu da Allah, da rungumar kyawawan ɗabi’u da za su inganta zaman lafiya, haƙuri da fahimtar juna a tsakanin al’umma.

Gwamnan ya kuma jaddada cewa ƙalubalen da ake fuskanta a yau na buƙatar jama’a su yi koyi da darussan Hijira ta hanyar guje wa rarrabuwar kawuna, ƙiyayya da son kai, tare da rungumar haɗin kai da aiki tare domin ci gaban al’umma.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!