Labarai
Majalisar wakilai ta ja hankalin jami’o’in kan karin kudin makaranta
Majalisar wakilan Nijeriya ta gargadi jami’o’in kasar nan da kada su fake da sabon tsarin bada rancen kudin karatu ga dalibai wajen karin kuɗaɗen makaranta.
Wannan ya biyo bayan kudirin da ɗan majalisa Terseer Ugbor na jam’yyar APC daga jihar Benue ya gabatar a zaman majalisar.
A cewar sa tsarin bada rancen kuɗin karatu kamar yadda yake a mafiya yawan ƙasashen duniya tsari ne mai kyau dake baiwa masu ƙaramin ƙarfi damar samun ilmi, wadda ke zama ƙashin bayan ci gaban al’umma da tattalin arzikin ƙasa.
Don haka ne ma ya buƙaci majalisar wakilan tarayyar da ta tabbatar da aiwatar da tsarin bisa ƙa’ida kamar yadda aka shirya.
Rahoton : Asma’u Muhammad Sani
You must be logged in to post a comment Login