Labarai
Majalisar wakilai ta nemi gwamnati ta haramta amfani da Queen Premier
Majalisar wakilai ta Nijeriya ta bukaci gwamnatin tarayya da sauran kananan hukumomi da su haramta amfani da wani shahararren littafin karatun yara a firamare mai suna “Queen Premier” a makarantun kasar nan.
‘Yan majalisar sun bukaci gwamnatin tarayya da jihohi da kuma kananan hukumomi da su hana amfani da littafin saboda ya kunshi kalmomi kamar “gay” da “eros” dama wasu da ake ganin na “batsa” ne.
Kiran haramcin ya biyo bayan amincewa da kudirin da Sulaiman Gumi na jam’iyyar PDP, a jihar Zamfara ya gabatar a ranar Alhamis din nan yayin zaman majalisar.
Gwamnatin jihar Kano ce dai tun da fari a kwanakin baya ta fara haramta amfani da littafin a dukkan makarantun da ke fadin jiharta.
You must be logged in to post a comment Login