Labarai
Majalisar wakilai ta nemi INEC ta dawo da rarar kudin zaben 2015
Majalisar wakilai ta bukaci hukumar zabe ta kasa INEC da ta dawo da kudaden da aka ware mata don gudanar da babban zaben kasa da aka gudanar a shekarar dubu biyu da goma sha biyar, wanda ya kai naira biliyan saba’in da uku.
Kwamitin kula da asusun gwamnati na majalisar wakilai, ya ce, ofishin akanta janar na kasa a waccan lokaci, ya sakarwa hukumar ta INEC da kudade da suka kai naira biliyan saba’in da uku don gudanar da babban zaben kasa a shekarar ta 2015.
Sai dai ya ce wannan kudaden basa cikin naira biliyan arba’in da biyar wanda tun farko aka amincewa hukumar ta INEC ta kashe don gudanar da zabukan.
Shugaban kwamitin kula da asusun gwamnati na Majalisar ta wakilai Wole Oke tare da sauran mambobin kwamitin sun bukaci hukumar ta INEC da ta dawo da wadannan kudade.
Majalisar ta kuma zargi ofishin akanta janar na kasa a waccan lokacin da yin gaban kansa wajen fitar da kudaden ba bisa ka’ida ba.
A bangare guda majalisar wakilan ta kuma bukaci akanta janar na kasa da ya dawo da wasu kudade da suka kai naira biliyan goma sha shida da miliyan dari tara wanda wani bangare ne na naira biliyan talatin da shida da miliyan dari tara da aka amince hukumar ta INEC ta kashe a shekarar dubu biyu da goma sha biyar, amma sai ofishin na akanta janar ya sakarwa INEC din da naira biliyan goma kacal.
You must be logged in to post a comment Login