Kiwon Lafiya
Majalisar wakilai ta tuhumi babbar jami’a mai kula da shirin Npower
Majalisar wakilai ta tuhumi babbar jami’a mai kula da shirin gwamnatin tarayya na samar da aikin yi ga matasa NPOWER Hajiya Maryam Uwais kan rashin sanya dukkannin masu ruwa da tsaki cikin shirin.
Shugaban kwamitin yaki da fatara na majalisar Muhammed Ali Wudil ne yayi wannan korafi lokacin da Hajiya Maryam Uwais ta jagoranci jami’an shirin, domin kare kunshin kasafin kudin su gaban kwamitin na majalisar wakilai.
A cewar Muhammed Ali Wudil, mambobin majalisar suna wakiltar dukkan-nin al’ummar kasar nan ne a don haka ba daidai bane a ce za a gudanar da shirin batare da tuntubar su ba, yana mai cewar, da an yi haka matsalolin zabar wadanda za su ci gajiyar shirin da ake fuskanta a yanzu da ba a same su ba.
Ya ce a yanzu kididdigar da suka samu ya nuna cewa yawancin al’ummar wasu yankunan kasar nan ne suka fi amfana da shirin.
Da take mai da jawabi Hajiya Maryam Uwais ta ce sun koyawa ma’aikatan gwamnati da kuma jami’an kananan hukumomi domin samun nasarar shirin.