Kiwon Lafiya
Majalisar wakilai ta umarci rundanar yan sanda da ta fice daga shalkwatar kungiyar Peace corps
Majalisar Wakilai ta umarci Rundunar ‘yan-sandan kasar nan ta fice daga shelkwatar kungiyar tsaro ta Peace Corps da ke birnin tarayya Abuja cikin Sa’o’i 48, da suka garkame tun ranar 28 ga watan Fabarairun bara.
Kwamitin Majalisar kan korafe-korafen al’umma ne ya bada wannan umarni a jiya Talata bayan takfa muhawara yayin jin ra’ayin jama’a bisa korafin da gamayyar kungiyoyin tabbatar da adalci da daidaito ta shigar gaban majaisar tana zargin babban Sufeton ‘yan-sandan kasar nan Ibrahim Idris ranar 25 ga watan Janairun bana.
Gamayyar kungiyoyin mai taken Coalation of Civil Society Organisations for Justice and Equity, sun zargi Ibrahim Idris da bijirewa umarnin babbar kotun tarayya ta Abuja cikin watan Nuwamban bara, da ta baiwa ‘yan-sanda umarnin bude Ofishin.
Yayin taron jin r’ayin jama’ar shugaban kungiyar ta Peace Corps Dickson Akoh ya shaidawa kwamitin cewa sun samu hukunce-hukuncen kotuna 12 da suka nuna cewa yunkurin ‘yan-san ya saba ka’ida, inda ya buga misali da hukuncin alkalai biyu Mai Shari’a Gabriel Kolawale da mai Shari’a John Tsoho.