Kiwon Lafiya
Majalisar wakilai ta yi barazanar kama shugaban hukumar NEMA Mustapha mai Haja
Majalisar wakilai ta yi barazanar kama shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta Najeriya NEMA Alhaji Mustapha mai Haja, sakamakon gaza bayyanar sa karo na 3 gaban kwamitin zauren majalisar da ke kula da bada agajin gaggawa.
Da yake jawabi yayin taron jin ra’ayoyin jama’a a jiya Alhamis shugaban kwamitin Ali Isah ya ce Mai haja ya ki martaba kiran da zauren majalisar ya yi masa karo uku a jere.
Ya kuma ce mai haja naya aika musu da sakon ba zai samu damar amsa gayyatar ba har sai ya rage saura mintuna 30 a zauna ko kuma a wasu lokutan ma sai sun zauna.
Tun da farko kafin fara taron jin ra’ayoyin jama’ar kwamitin ya umarci babban bankin kasa CBN da kuma ofishin akanta Janar na kasa da kuma ma’aikatar kudi ta kasa da sauran masu ruwa da tsaki da su fitar da bayanin yadda aka kashe naira bilyan biyar da miliyan dari shida da aka fitar wa hukumar bada agajin gaggawa ta kasa.