Labarai
Majalisar wakilai taki amincewa da karin firashin man fetur
Shugaban marasa rinjaye na majalisar wakilai Ndudi Elimelu ya ce baza su amince da karin farashin man fetir da aka samu a baya-bayan nan ba, wanda ya tashi daga naira dari da arba’in da takwas zuwa dari da Hamsin da daya a kowacce lita.
Hakan na cikin wata sanarwa ce da shugaban marasa rinjayen ya sanyawa hannu, wadda ke dauke da kin amincewar su sakamakon yadda karin zai haifar da tashin farshin kayayyakin masarufi.
Ndudi Elimelu wanda dan majalisar tarayya ne daga jihar Delta, ya ce tashin farashin man fetur din zai kara ta’azzara tattalin arzikin kasar nan.
Bayan da aka yi karin farashin fetur da wuta kayan gwari bai sauya ba – kungiya
Abun da ya sanya NUPENG dakatar da rarraba man fetur a Legas
Mr Ndudi Elumelu ya kara da cewa, sakamakon hakan ne bangaren marasa rinjaye na majalisar wakilai suka ki amincewa da karin farashin man fetir din saboda la’akari da yadda ‘yan Najeriya ke rayuwa mai tsada a wannan lokaci.
You must be logged in to post a comment Login