Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Coronavirus

Babu wani mataimakina da ya kamu da corona – Buhari

Published

on

Fadar shugaban kasa ta musanta labarin da ake yadawa cewa guda daga cikin masu taimakawa shugaba Buhari wato Sarki Abba ya kamu da cutar Corona.

Hakan na cikin sanarwar da mai baiwa shugaban kasar shawara kan kafofin yada labarai Malam Garba Shehu ya fitar.

Ta cikin sanarwar Garba Shehu ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi watsi da wannan jita-jita, yana mai cewa wannan labara ne da bas hi da tushe ballantana makama, yana mai cewa wasu marasa kishin kasane kawai suka kirkiri labarin don haifar da fargaba a zukatan mutane.

Sanarwar ta ce labarin da ake yadawa cewa Sarki Abba wanda makausanci ne ga shugaba Buhari kuma mai taimakwa shugaban kasar kan harkokin cikin gida ya kamu da cutar lamarin da ya sanya ba’a ganin gilmawar sa tsahon makkoni biyu ba gaskiya bane.

Sanarwar dai ta bukaci ‘yan kasar nan da su yi watsi da jita-jitar don kuwa an shirya ta ne da wata manufa mara amfani.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!