Connect with us

Labarai

Majalisar Wakilai za ta kafa kwamitin binciko kadarorin gwamnatin Tarayya

Published

on

Majalisar Wakilai za ta kafa kwamitin wucin gadi domin binciko kadarori mallakar gwamnatin tarayya da suka hada da filaye da gine-gine da aka yi watsi da su a faɗin ƙasar, da darajarsu ta kai sama da Naira tiriliyan 20.

Wannan ya biyo bayan amincewa da wani kudiri na gaggawa wanda Shugaban marasa rinjaye na majalisar, Kingsley Chinda dan jam’iyyar PDP daga jihar Rivers, ya gabatar a zaman majalisar na ranar Laraba.

Chinda, ya ce, dole a yi binciken don hana ƙarin ɓarnatar da albarkatun jama’a da kuma tabbatar da dawo da kadarorin ƙasa masu mahimmanci.

Ya yi nuni da rahoton 2021 da Cibiyar Binciken kasa ta Nijeriya ta fitar, wanda ya gano kimanin filaye da gine-ginen gwamnatin tarayya 11,866 da aka yi watsi da su a duk faɗin ƙasar.

Daga cikin manyan kadarorin da ɗan majalisar ya lissafa akwai Cibiyar Sakatariyar Tarayya da ke Ikoyi, Legas; Ginin Otal na Ƙasa da Ƙasa na Nijeriya, a Sulejan  Jihar Neja; Millennium Tower, Abuja; Ginin Hukumar Haraji ta Tarayya a Jihar Abia; Hedikwatar Dakin karatu na Ƙasa, Abuja; Kamfanin Masana’antar buga Labarai na Nijeriya, Kaduna; Ginin Masaƙa ta Kaduna; da Kamfanin Narka Alluminium na Nijeriya, Jihar Delta.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!