Kiwon Lafiya
Majalisar zartarwa ta amince da kashe biliyan 27 a ayyukan raya kasa
Majalisa zartaswa ta amince da fitar da Naira Billiyan 27 don sayan buhu-hunan Gero da kayayaykin wuta lantarki da kuma gyara wasu daga cikin Titunan Birnin tarayya Abuja.
Ministan Noma da albarkatun kasa Audu Ogbeh ne ya bayyana haka, a zaman majalisar na jiya, wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta.
Audu Ogbeh ya kuma ce, an ware Naira Billiyan Tara da milliyon hudu da nufin sayan Gero tan Dubu sittin baya ga amince da sayan tan din Masara Dubu sitin da daya da Dawa da kuma Ridi, don samar da iri da za a suka a damar bana.
A nasa banagaren Ministan wutan lantarki da gidaje Babatunde Raji Fashola ya ce majalisar ta kuma amince da fitar da Naira Biiliyon Bakwai da Milliyon daya, don gyara titin Abaji mai hannu biyu da wata gada, duk a birnin tarraya Abuja don saukaka masu ababen-hawa zirga-zirga.