Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Majalisar zartaswa ta amince da kashe biliyan 4 domin yin wasu ayyuka 3

Published

on

Majalisar zartaswar Najeriya, ta amince a kashe Naira biliyan hudu domin gudanar da wasu muhimman ayyuka guda uku.

Ayyukan dai sun hada da gina ofisoshin shugabannin jami’ar jihar Osun da Osogbo da kuma na jami’ar Tarayya ta Lokoja, sai kuma samar da tirke eriyar rediyo a hukumar kula da Ilimin makiyaya ta Najeriya.

Ministan Ilimi Malam Adamu Adamu, ne ya bayyana a ganawarsa da manema labaran fadar shugaban kasa jim kadan bayan kammala taron majalisar wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta jiya Laraba a birnin tarayya Abuja.

Malam Adamu Adamu, ya ce, za a yi gine-ginen jami’ar ta jihar Osun ne a kan kudi sama da Naira biliyan 2 cikin wa’adin mako 76 da aka baiwa kamfanin.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!