Labarai
Majalisar zartaswa ta amince da ware fiye da Tiriliyan 68 don samar da lantarki a jamio’i da asibitoci

Majalisar zartaswa ta Najeriya, ta amince da ware sama da Naira Tiriliyan 68 domin ayyukan samar da wutar lantarki a jamio’i da asibitocin koyarwa a faɗin ƙasar.
Ministan makamashi Adebayo Adelabu, ne ya bayyana hakan a ƙarshen taron majalisar a jiya alhamis, wanda shugaban ƙasa Bola Tinubu ya jagoranta.
Adebayo, ya ce, za a yi amfani da kuɗin ne domin taimakawa wajen samar da wuta a jam’ioi da asibitocin koyarwa guda 8 a faɗinNajeriya.
Ciki har da Jam’iar jihar Legas, da Jam’iar Ahmadu Bello da ke Zaria, sai Jami’ar Obafemi Awolowo da ke Ile-ife.
Sai kuma Jam’iar Najeriya da ke Nsukka, da Jami’ar Ibadan, da kuma Jam’iar Calabar da sauransu.
Ya kuma ce ana sa ran kammala ayyukan samar da wutan nan da watannin 7 zuwa 9.
You must be logged in to post a comment Login