Labarai
Makarantu a Kano zasuci gaba da zama a rufe- kwamishinan Ilimi
Gwamnatin Kano ta ce za ta dauki tsatstsauran mataki ga makarantun da suka bude, yayinda ake rade-radin bude makarantu a jihar.
Idan za a iya tunawa a baya-bayan nan ne kwamitin kar-ta kwana kan annobar Covid-19 ya ce an bawa jihohi dama su bude makarantu bisa yarjejeniyar bin dokokin yaki da annobar Covid-19.
Amma kwamitin yace daliban da aka bawa damar komawa makaranta sune ‘yan aji shida a makarantun firamare da kuma ‘yan aji uku da aji shida a makarantun sakandire.
Sai dai gwamnatin Kano ta ce har yanzu bata yanke ranar da za a koma makaranta ba, yayinda gwamnatin Legas ta ce malamai zasu fara shiga aji ranar uku ga watan Agusta.
A zantawar da Freedom Radio ta yi da kwamishinan ilimi na jihar Kano, Sanusi Sa’idu Kiru, yace shakka babu za su dauki tsatstsauram mataki ga duk malamin da aka gano ya shiga aji da sunan koyarwa.
A cewarsa jihar Kano ce kan gaba a yawan daliban da zasu zana jarabawar kammala makaranta sakandire, da kuma aji na uku a makarantun sakandire a Najeriya.
You must be logged in to post a comment Login