Connect with us

Labarai

Gwamnatin Legas za ta bude makarantu a watan Agusta

Published

on

Gwamnatin jihar Legas ta sanar da cewa za ta bude makarantu a ranar uku ga watan Agustan 2020.

Sai dai gwamnatin ta ce daliban aji uku da kuma shida ne na makarantun sakandire aka yarjewa su koma makaranta.

Gwamnatin jihar ce ta bayyana hakan a shafinta na Twitter, inda ta ce an bawa daliban damar komawa karatu domin rubuta jarabawa.

A baya-bayan nan ne gwamnatin tarayya ta bayar da umarnin a bude makarantu, domin bawa dalibai damar rubuta jarabawarsu ta fita.

Daga cikin daliban da ake sa ran za su koma karatu, akwai daliban aji shida a makarantun firamare, sai daliban aji uku da aji shida a makarantun sakandire.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!