Labarai
Makarantu masu zaman kan su dole su bi ka’idojin bude makarantu – NUT
Hadaddiyar kungiyar malamai ta kasa ta bukaci makarantu masu zaman kansu da su bi dokokin da aka shimfida wajen kare dalibai daga kamuwa daga cutar COVID- 19 ya yin da za’ bude makarantu nan bada jimawa ba.
Shugaban kungiyar ta kasa Nasir Idris ya bayyana hakan wanda ya sami wakilcin sakataren kungiyar Idris Amba ya ce karamin ministan ilimi Chukwuemeka Nwajiuba na cewa gwamnatin tarayya na shirye – shiryen gudanar da bikin ranar malamai ta duniya wanda za’a yi a ranar 5 ga watan Okotoba mai kamawa.
A ya yin taron ministan ya sheda cewa a ya yin bikin na bana za’a tsamo tare da baiwa malaman da suka fi kowa kwazo daga kananan hukumomi dari 774 na fadin kasar nan.
You must be logged in to post a comment Login