Labarai
Malam Aminu Kano ya cika shekaru 40 da rasuwa
-
Tsarin siyasar da ake gudanarwa a yanzu ya sha bamban da wadda marigayi Malam Aminu Kano ya yi
-
Babban amfanin dimukuradiyya shi ne a samar da ci gaba.
Cibiyar bincike da horaswa kan harkokin dimukuradiyya ta jami’ar Bayero da ke gidan Mambayya a Kano ta ce, tsarin siyasar da ake gudanarwa a yanzu ya sha bamban da wadda marigayi Malam Aminu Kano ya yi a zamanin rayuwarsa.
Daraktan cibiyar Farfesa Habu Muhammad Fagge ne ya bayyana hakan a zantarwarsu da Freedom Radio a safiyar yau.
Tattaunawar ta mayar da hankali ne kan shirye shiryen taron tunawa da margayi Malam Aminu Kano wanda ya cika shekara 40 da rasuwarsa.
A gefe guda kuma, wani kwararren mai bincike a wannan cibiyar ta Mambayya Malam Abdullahi Usman Kofar Na’isa ya ce, “Babban amfanin dimukuradiyya shi ne a samar da ci gaba”.
Dukkanin bakin sun bayyana irin gudumawar da margayi Malam Aminu Kano ya bayar a fanin siyasar dimokradiyya a matsayin wadda ba za a taba mantawa da it aba.
Rahoton: Bara’atu Idris Garkuwa
You must be logged in to post a comment Login