Connect with us

Manyan Labarai

Malaman jami’a da basu yi Rijistar IPPIS ba, kada su sa ran karbar albashi.

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ce mambobin kungiyar manyan malamn jami’a ta kasa ASUU da suka ki yin biyayya ga shiga tsarin Gwamnatin na IPPIS kada su tsammacin samun albashin su.

Ministar kudi ta tarayya Hajiya Zainab Ahmed ce ta bayyana hakan da yammacin jiya Alhamis lokacin da ake bikin bude taron karawa juna sani na bana wanda aka shiryawa manyan jami’an kula da harkokin kudi da binciken su na ma’aikatar a nan Kano.

Hajiya Zainab ta kuma ce kaso 55 na malam jami’ar basu yi rajistar da tsarin ba tana mai karin bayanin cewa daga lokacin da aka bijiro da tsarin an samu damar bankado ma’aikatan bogi fiye da dubu 70.

Labarai masu alaka.

Ba za mu shiga tsarin IPPIS ba -ASUU

Tsarin albashi na IPPIS: Kungiyar Malaman Jamioi na Jayayya da Gwamnatin tarayya.

Ta ce Gwamnatin tarayya ta bijiro da tsarin na IPPIS ne don tabbatar da cewa halastattun ma’aikatan gwamnati ne kadai ke karbar albashi ba wai na bogi ba.

Daga nan kuma sai ta yabawa Gwamnatin tarayya kan yadda ta ke bijirowa da tsare-tsare manaragta don inganta tsarin aikin gwamnati, tana mai cewa hakan na rage ha’inci da sn zuciya a yayin tafiyar da aikin gwamnati a kasar nan.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Labaran Kano

 An tantance mutane 46 a Kano kan Coronavirus

Published

on

Ma’aikatar lafiya ta jihar Kano ta ce, sakamakon gwajin da ta yiwa mutune arba’in da shida na cutar Covid-19 ya tabbatar ba sa dauke da cuta yayin da kuma take dakwan sakamkon mutum 4.

Kwamishinan lafiya na jihar Kano Dakta Aminu Ibrahim Tsanyawa ne ya bayyana hakan ya yin zantawa da manema labarai daya gudana a yau laraba.

Kwamishinan ya kara da cewar har hanzu jihar Kano bata da ko mutum guda dauke da cutar ta Corona ba.

Dakta Aminu Ibrahim Tsanyawa ya kara da cewar ma’aitakar lafiya ta yi tsare-tsare da zata dauki matakan dakile cutar ya sanya ta karawa ma’aikata hutun  makwanni biyu.

Wakiliyar mu Aisha shehu Kabara ta ruwaito cewar Kwamishinan ya sake nanata cewar duk  wadanda aka yi wa gwajin basa dauke da cutar ta Covid19.

Continue Reading

Manyan Labarai

A Yanzu -Yanzu : gobara ta tashi a Ofishin akanta na kasa

Published

on

Babban ofishin  Akanta Janaral na kasa  ya kama da wuta wanda yanzu haka wutar na ci gaba da mamayar ofishoshi da dama.

Ofishin mai sunan  “Treasury House” na kusa da Babbar Shalkatar ‘Yan sanda ta kasa ,dake Garki a birnin tarayya Abuja.

Jaridar punch ta rawaito cewa a safiyar yau ne wutar ta tashi inda ta fara mamaye ofisoshi da dama.

Continue Reading

Labarai

Gwamnatin jihar Jigawa ta fara biyan ‘yan Fansho

Published

on

 

Gwamnatin jihar Jigawa ta fara biyan yan fansho su kimanin 570 sama da naira biliyan daya.

An raba mutanen zuwa rukuni-rukuni saboda kaucewa cunkoson don rage yaduwar corona da ke yiwa duniya barazana a halin yanzu.

Shugaban hukumar fansho ta jihar Jigawa, Alhaji Hashimu Ahmad Fagam ne ya bayyana haka a jiya Talata lokacin da yake bayyana irin ayyukan hukumar fansho a jihar ta Jigawa.

Alhaji Hashimu Ahmad Fagam ya ce tsofaffin ma’aikatan da za su ci gajiyar shirin sun hada da wadanda suka fito daga jihar da kananan hukumomi a matakin farko.

Ya kuma ja hankalin tsofaffin ma’aikatan da suka samu hakkokin su da su yi amfani da su ta hanyar da ta dace.

Shugaban ya kuma ce wadanda  suka rasu da kuma sauran balas na wadanda suka yi ritaya za a biya kudin a matakin da ake ciki.

Continue Reading

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 316,595 other subscribers.

Trending

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!