Connect with us

Manyan Labarai

Tsarin albashi na IPPIS: Kungiyar Malaman Jamioi na Jayayya da Gwamnatin tarayya.

Published

on

Tun ranar takwas ga watan Oktoban da muke ciki ne shugaban kasa Muhammadu Buhari  a lokacin da yake gabatar da kasafin kudi na shekarar 2020 yace daga ranar 31 ga watan Oktoba kowanne ma’aikacin gwamnatin tarayya sai ya shiga tsarin nan na biyan albashi da ake kira da IPPS.

Shugaba Buhari yayi wannan jawabi sakamakon yadda ake ganin cewa tsarin na IPPS mataki ne da gwamnatin tarayya take da shi na biyan albashin maaikatan ta ba tare da wata matsala ko kadan ba da ta hada da magance cin hanci da rashawa.

A da, wasu ma’aikatu ne dai na gwamnatin tarayya ake biya albashi ta tsarin bai daya da ake wa lakabi da IPPIS, inda wasu bangarori suka dade suna kokawa akan haka, musamman ma bangaren jami’an tsaro da suka hada da sojoji da hukumar ‘’yansanda da  hukumar gyara halaye ta Najeriya wato NCS da sauran gurare.

Wasu bangarorin na Gwamnatin tarayya musamman bangaren jami’an tsaro sun koka da yadda suke samun albashin su kafin a saka su a tsarin na IPPIS ,har sai da gwamnatin tarayya ta saka hukumomin tsaron a tsarin na IPPIS, sannan su ka samu sauki  wajen  karbar albashin nasu .

A makwannin nan da muke ciki kungiyar malaman jami’oi ta kasa wato ASUU ta  ja daga da gwamnatin tarayya na  cewa su ba zaa saka malaman jami’a  a tsarin na IPPIS ba.

Wannan dambarwa dake faruwa tsakanin Gwamnatin ta tarayyar Najeriya da malaman jamio’in kasar nan na neman barin baya da kura, inda ita gwamnatin tarayyar ta Najeriya ta ja daga, inda tace lallai sai kowanne ma’aikacin gwamnatin ta tarayyar Najeriya ya shiga tsarin na biyan albashi ta IPPIS.

A satin nan da muke ciki ne dai kungiyar Malaman jamio’in ta Najeriya ta rika tattaunawa da sauran jami’an gwamnatin tarayya a game da hanyar biyan albashin na bai daya wato IPPIS amma samun matsaya yaci tura har yanzu.

Bayanai da ke fitowa na nuni da cewa kungiyar ta ASUU na shirin fadawa yajin aiki muddin Gwamnatin tarayya ta dage a saka su a tsarin biyan albashin na IPPIS ,ita ma kuma gwamnatin tarayya ta cigaba da kafewar cewa babu gudu babu ja da baya a game da  saka kowacce ma’aikatar gwamnatin tarayya a tsari na biyan albashi na IPPIS.

Ko a kwanannan ma , sai da ministar kudi Hajiya Zainab Ahmad tace saka Malaman jamia a tsarin na IPPIS umarni ne na shugaba Muhammadu Buhari.

A kwai dai bayanai dake nuna cewa malaman jamiar ta Najeriya na koyarwa a jamio’i da dama ,bayan jamio’in su na asali, hakan ta sa ake ganin saka malaman jamiar a tsarin na IPPIS abune da zai hana su karbar albashi da yawa a maimakon albashin su na asali.

 

Manyan Labarai

Tarbiyantar da ‘ya’ya ya wajaba kan iyaye- Sarkin Kano

Published

on

Mai martaba sarkin Kano Malam Muhammad Sunusi na biyu, ya ja kunnan iyaye wajen tabbatar da suna sauke nauyin da All- subhanawu-wata’ala ya dora a kansu na tarbiyantar da ‘ya’yansu bisa koyarwar addinin Islama.

Sarkin na bayyana hakan ne yau yayin bikin kaddamar da faifan CD na karatun Al-qur’ani mai girma na ruwayar Qalun da Gwana Nafisatu Yusuf Abdullahi ta gabatar a dakin taro na Mumbayya dake Gwammaja.

Muhammad Sunusi ya kuma ce ba dai-dai bane iyaye su rinka turo iyayen su cikin gari da sunan almajirci ba tare da sun baiwa malaman da za su koyar da ‘ya’yan na su abincin da za su ciyar da su ba, ta yadda hakan kansa ‘yaran gararamba a gari wajen neman abinci da za su ciyar da kansu.

Da take na ta jawabin gwana Nafisa Yusuf Abdullahi, data gudanar da karatun al-qur’ani na ruwayar ta Qalun a faifan CD, jan hankalin ‘yan uwanta mata tai wajen neman ilimin addinin Islama da na zamani tare da kiran al’umma wajen tallafawa makarantar da wajen zama nata na dindin din.

Kyautatawa malamai ya zama wajibi- Shekarau

Zulum- ya baiwa malamai 30 kwangilar addu’o’i a kasa mai tsarki

Mahukunta su mai da hankali kan al’umma -Limami

Wakilin mu Abubakar Tijjani Rabi’u ya rawaito cewa, mai alfarma sarkin musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar na uku da sanatan kano ta tsakiya Malam Ibrahim Shekarau da malamai da ‘yan siyasa da dalibai da dama ne suka halarci taron kaddamar da faifan CD na kira’ar ta Qalun.

 

Continue Reading

Labaran Kano

Al’umma na da damar yin kiranye ga wakilan su- Barista Turmuzi

Published

on

Wani lauya a nan kano, Barista Sale Muhammad Turmuzi, ya ce, jama’a suna da ‘yancin yin kiranye ga wakilansu da ke jiran hukuncin kotu, bayan daukara kara a kotu ta gaba, bisa wani zargin cin hanci da rashawa.

Barista Sale Muhammad Turmuzi, ya bayyana hakan ne ta shirin Muleka mu gano na musamman na nan tashar freedom Rediyo da ya gudana a daren jiya.

Batista Sale Turmuzi, ya kara da cewa, a tsarin yadda doka ta tanada, duk wani dan majalisa da ya rasa kaso daya bisa uku na zaman majalisa zai iya rasa kujerarsa matukar bashida kwararan hujjoji.

A daina siyasar uban gida a Najeriya domin cigaban demokradiyya -Farfesa Kamilu

Shugaba Buhari yayi ganawar sirri da wasu tawagar yan siyasa daga Kano

Sale Muhammad Turmuzi, ya kuma ce, an samu gagarumin ci gaba a bangaren yaki da cin hanci da rashawa a fadin kasar nan musamman a bangaren shari’a, bisa yadda ake ganin Kotuna a wannan lokaci suna yanke hukuncin da ke turawa da masu rike da mukaman siyasa zuwa gidan gyaran hali.

Muhammad Sale Turmuzi, ya kuma nanata cewa, zartas da hukuncin zaman gidan gyaran hali kan tsoffin gwamnoni kuma sanatoci masu ci kan cin hanci zai taimaka gaya wajen karfafa mulkin dimukuradiyya.

Continue Reading

Labarai

Shugaba Buhari ya jajantawa alummar Garkida

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jajantawa al’ummar kauyen Garkida na jihar Adamawa da kungiyar Boko Haram ta kaiwa hari.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban mataimaki na musamman kan harkokin yada labarai Garba Shehu ya fitar jiya a birnin tarayya Abuja.

Ta cikin sanarwar, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce shakka babu sojojin kasar nan sun mai da hankali kan rage wa mayakan Boko Haram karfi a yankunan arewa maso gabashin kasar nan.

Shugaba Buhari ya ce ya zama wajibi a yabawa jami’an tsaron kasar nan kan yadda suke aiki ba dare ba rana wajen tabbatar da zaman lafiya.

Yaki da cin hanci da rashawa bana Buhari ba ne- Ministan Ruwa

Buhari Bai Damu Da Harkokin Lafiya Ba-Likitocin Yara

Shugaba Buhari ya gana da sufeton yan sanda ta kasa kan arangamar yan Shi’a

Muhammadu Buhari ya kara da cewa, nan da wani dan lokaci Gwamnati zata kaddamar da kamfe kan yakar ta’addanci.

Shugaban kasa ya kuma yi kira ga al’ummar kasar nan wajen ci gaba da baiwa jami’an tsaro goyon baya na kare dukiya da tsaron lafiyar ‘yan kasar nan.

Continue Reading

Now Streaming

Trending

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!