Labarai
Mamakon ruwa da yin gine-gine a kan magunai ne ya janyo ambaliyar Maiduguri- NEMA

Hukumar bayar da agajin gaggawa da Najeiya NEMA, ta ce mamakon ruwan sama da kuma yin gine-gine a kan magunan ruwa ne ya janyo ambaliyar da ta afku a birnin Maiduguri a bayabayan nan.
A jiya Laraba ne aka samu rahotonni ambaliya a wasu unguwannin birnin na Maiduguri da ke jihar Borno a yankin ƙaramar hukumar Jere sakamakon ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da aka shafe tsawo sa’o’i uku ana tafkawa.
Ta cikin wata sanarwa da shugabar hukumar ta NEMA, Zubaida Umar ta wallafa a shafinta na Facebook ta danganta ambaliyar da rashin bin tsarin gine-gine.
Hukumar ta NEMA ta kuma ce, jami’anta tare da haɗin gwiwar sauran hukumomi sun taimaka wajen ceto mutanen da ambaliyar ta rutsa da su tare da rage illar da ta haifar.
You must be logged in to post a comment Login