Labarai
Mamakon ruwa sama da iska sun lalata gidaje da dama a Makarfi

Ruwan sama mai ƙarfi wanda ke dauke da iska, sun lalata gidaje da dama a garin Makarfi na Jihar Kaduna, lamarin da ya jefa mazauna yankin cikin halin zullumi.
Shugaban Ƙaramar hukumar ta Makarfi, Moh’d Sabon Gari, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi.
Shugaban ya bayyana cewa, mafi yawan waɗanda lamarin ya shafa talakawa ne, yana mai cewa majalisar karamar hukumar ta haɗa kai da hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar domin tallafa musu.
Ya kuma yi kira ga shugabannin al’umma da su wayar da kan jama’a kan illar zubar da shara a cikin magudanan ruwa domin kauce wa irin wannan iftila’i a gaba.
You must be logged in to post a comment Login