Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Man United ta samu tikitin zuwa Champions League

Published

on

Manchester United, ta kai bantan ta da kyar a kokarin neman tikitin zuwa gasar kofin Zakarun Turai ta Champions league , bayan samun nasara a wasanta da abokiyar burminta ta Leicester City.

A wasan karshe, kuma na 38 a gasar kakar wasanni ta bana,2019/2020, Manchester ta samu nasara da ci biyu da nema a filin wasa na Kingpower Stadium, dake birnin na Leicester.

Bayan tafiya hutun rabin lokaci a zagaye na biyu, dan wasa Bruno Fernandez ya zura kwallo a minti na 71 a bugun daga kai sai mai tsaron gida, bayan da ‘dan wasa Martial ya samo bugun.

Ana gab da tashi a wasan ne kuma, cikin minti na 90 mai tsaron gida na Leicester City , Kasper Schemiechel ya yi kuskuren turawa dan wasan gaba na tawagar Manchester wato Jesse Lingard kwallo, wanda take ya yi amfani da damar wajen zura kwallo ta biyu, hakan ya tabbatar da kasancewar su a gurbi na hudu haka kuma na karshe a kungiyoyin da za su wakilci kasar a gasar Champions league na shekarar mai zuwa, bayan samun maki 66.

*AHT*

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!