Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Manchester United ta dauki dan wasan Ajax Donny van de Beek

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United dake kasar Ingila ta tabbatar da daukan dan wasan tsakiyar kungiyar kwallon kafa ta Ajax, Donny van de Beek.

A yau Laraba ne dai kungiyar ta United ta tabbatar da hakan a shafin ta na Internet.

Manchester dai ta sayi dan wasan Donny van de Beek kan kudi Yuro miliyan 34.

Kuma shi ne dan wasa na farko da kungiyar karkashin mai horarwar ta Ole Gunnar Solskjaer ta fara dauka, domin tunkarar kakar wasanni mai zuwa.

Dan wasan na Ajax dai Van de Beek ya taimakawa kungiyar tasa wajen zuwa wasan dab dana karshe a shekara ta 2019 a gasar cin kofin zakarun turai Champion League.

Ya dai sanyawa Manchester United kwantaragin shekaru biyar ne, domin buga mata wasanni.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!