Connect with us

Labaran Wasanni

US Open 2020: Serena Williams ta doke Kristie Ahn

Published

on

Serena Williams na ci gaba da fafutukar neman kambun gasar kwallon tennis ta Grand Slam karo na 24.

Williams dai ta yi nasarar doke ‘yar wasar kasar Amurka Kristie Ahn da ci 7-5 da kuma 6-3.

‘Yar wasan mai shekaru 38 ta fuskanci kalubale a zagaye na farko da na biyu, kafin daga bisani ta yi nasara kan ‘yar wasan.

Yanzu haka dai Serena Williams na rike da kambun kwallon tennis na Grand Slam 23, ya yin da take kokarin zuwa kan-kan-kan da ‘yar wasa, Margaret Court da ke da 24.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!