Kasuwanci
Manoman Albasa sun tafka asarar Miliyoyin Naira sakamakon Iri maras inganci

Manoman Albasa a jihar Kano na ci gaba da koka wa bisa yadda suka tafka asarar Miliyoyin Naira bayan da aka sayar musu iri maras inganci da ya janyo musu wannan asara.
A zantawar wakilinmu Auwal Hassan Fagge, da wasu daga cikin manoman Albasar a Kano, sun bayyana cewa, an shigo da irin ne daga kasar waje inda suka saya tare da yin amfani da shi sakamakon yadda a bara irin Albasar ya yi tsada.
Haka kun sun kara da cewa, tsadar da Iri ya yi ne ya janyo wasu suka shigo da shi cikin kasar nan inda manoma suka saya tare da yafa shi a gonakinsu.
“ Ni kaina na tafka asara sosaisakamakon amfani da wannan iri, a ido za ka ga irin ba shi da maraba da wanda muka saba amfani da shi, sai dai bayan da lokacin girbi ya yi sannan muka gano cewa maras kyau ne”, inji wani manomi Alhaji Lawan Sulaiman Gurjiya.
Haka kuma ya kara da cewa, “ Na san wani makwabcina wanda ya kashe fiye da naira 500,000 a noman Albasa, amma wadda ya samu ko naira 10,000 ba ta kai ba, don haka muna kira ga gwamnati da duk masu ruwa da tsaki da su gudanar da bincike kan wadanda suka shigo da wannan iri tare da daukar mataki a kansu idan suna sane suka shigo da shi.
You must be logged in to post a comment Login