Addini
Manyan malaman Kano sun yi watsi da tsige Malam Ibrahim Khalil
Manyan Malaman Kano sun nesanta kansu da sanarwar tsige shugaban majalisar malamai na Kano da wasu suka bayar.
A cikin wata sanarwa da zauren haɗin kan Malamai da ƙungiyoyi na Kano ya aike wa Freedom Radio, ya ce ba da yawunsu aka ce an cire Malam Khalil ba.
Malaman da suka fitar da wannan sanarwar sune, Farfesa Musa Muhammad Borodo, Sheikh Ƙariballah Nasiru Kabara da Sheikh Abdulwahab Abdallah.
Sai Sheikh Ibrahim Shehu Maihula da Farfesa Muhammad Babangida da Imam Nasir Muhammad Nasir.
Sauran malaman su ne Dr. Bashir Aliyu Umar da kuma Dr. Ibrahim Mu’azzam Maibushira.
Babban sakataren haɗin kan zauren malamai da ƙungiyoyi na Kano Dr. Sa’id Ahmad Dukawa ne ya fitar da sanarwar.
Manyan Malaman sun yi watsi da wancan yunƙuri inda suka fito ƙarara suka bayyana cewa ba sa goyon bayan tsige Malam Khalil.
A ƙarshe sun bayyana yunƙurin tsige Malam Khalil a matsayin abin da ba zai haifar da zaman lafiya ba.
Ga sanarwar da suka fitar a ƙasa.
A ranar Litinin ne wani tsagi na Malaman ya sanar da tsige Malam Ibrahim Khalil tare da maye gurbinsa da Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan abin da ya janyo cece-kuce.
You must be logged in to post a comment Login