Labaran Kano
Marigayi Alhaji Ado Bayero ne ya kafa makarantar sakandiren Dambatta
Tsofaffin daliban makarantar Sakandiren Dambatta sun bayyana makarantar da cewa ta cika shekaru hamsin da kafuwa.
Shugaban kungiyar tsofaffin daliban makarantar Sakandiren ta Dambatta Alhaji Ubale Ibrahim Rano ne ya bayyana hakan lokacin da yake tattaunawa da filin Barka da Hantsi a shirin da makarantar take yi na bikin cika shekara hamsin da kafuwa.
Alhaji Ubale Ibrahim Rano ya kara da cewa a zamanin Native Authority lokacin da sarakuna ke da ikon kafa makarantu da sauran ayyukan al’umma marigayi sarkin Kano Ado Bayero ne ya kafa makarantar.
Yace bayan kirkirar Jahar Kano da shekaru uku mai martaba marigayi Alhaji Ado Bayero ya mika makarantar ga gwamnatin jihar Kano.
A nasa bangaren sakataran kungiyar tsofaffin daliban makarantar Barrister Dalhatu Ibrahim Daneji yace mafiya yawan ayyukan cigaba da makarantar take alfahari da shi a yanzu tsofaffin daliban makarantar ne suka aiwatar.
Yace daga cikin ayyukan da suka aiwatar akwai rage cunkoso a Ajujuwan makarantar daga dalibai 120 zuwa dalibai 70 a Aji.
Yace a halin yanzu akwai kujeru da suka kai dari biyar da za’a saka a ajujuwan.
Barrister Dalhatu Ibrahim Daneji ya kara da cewa a bikin da za su fara ranar 11 ga watan Disambar da muke ciki ana sa ran gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje zai halacci taron.
Daneji ya kara da cewa daliban da makarantar ta yaye kuma suka shahara akwai sarkin Hadejia Alhaji Adamu Abubakar Maje da tsohon babban sufeto na ‘yansandan Najeriya Suleiman Abba.