Labarai
Marigayi Audu Baƙo abin kwaikwayo ne ga gwamnonin yanzu – Dr Aisha Ni’ima
Malama a sashin nazarin tarihi a jami’ar Bayero da ke Kano ta ce, marigayi tsohon gwamnan Kano Audu Baƙo ya samarwa jihar Kano ci gaba mai ɗumbin yawa a zamanin mulkinsa.
Dakta Aisha Ni’ima Shehu ce ta bayyana hakan ta cikin shirin Barka da Hantsi na Freedom Radio a ranar Juma’a.
Malamar ta ce, ta rubuta littafin tarihin tsohon gwamnan Audu Baƙo ne domin irin cigaban da kuma rawar da ya taka wajen bunƙasa tattalin arzikin jihar Kano.
“Ya kawo ci gaba a ɓangaren ilimi domin shi ne ya assasa kwalejin share fagen shiga jami’a da kuma samar da ɗakin karatu na jihar da kuma rukunin masana’antu na Sharaɗa da challawa.”
Ta ƙara da cewa littafin mai taken Jihar kano a Mulkin Audu Bako na ɗauke da babi takwas waɗanda suka ƙunshi tahirin marigayin da kuma irin gudummawar da ya bayar a jihar kano da ƙasa ma najeriya.
You must be logged in to post a comment Login