Connect with us

Labaran Wasanni

Marseille ta bude makarantar wasanni a Najeriya

Published

on

Kungiyar kwallon kafa dake kasar Faransa wato Olympique Marseille za ta bude makarantar koyar da wasanni a cikin sashin koyon harkokin wasanni dake jami’ar Port Harcourt ta jihar Rivers a Najeriya.

Makarantar ta kunshi filin wasa da wajen motsa jiki da wajen guje-guje da tsalle-tsalle da asibiti da ajujuwa da ofis-ofis da gidan shakatawa da kuma otel.

A yanzu haka makarantar na da dalibai 200 wadan da zasu amfana da sabon tsarin bada horo a makarantar karshen watan Janairun sabuwar shekara mai zuwa.

Marseille dai na daya daga cikin manyan kungiyoyin kwallon kafa a nahiyar turai da take kokarin kawo ilimi da nishadi da kayatarwa tare da kuma gina rayuwar yan Afrika.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!