Labarai
Masarautar Ƙaraye ta mayar da Dagacin Madobawa kan kujerarsa
Masarautar Ƙaraye ta janye dakatarwar da ta yiwa Dagacin Madobawa a ƙaramar hukumar Ƙaraye Alhaji Shehu Musa.
An janye dakatarwar ne bayan da kwamitin da aka kafa domin gudanar da bincike kan duk wani zargi da ake yi wa Dagacin ya gabatar da rahoton sa.
Masarautar ta buƙaci Dagaci da ya ci gaba da gudanar da mulkin al’ummarsa cikin kwanciyar hankali da gaskiya da adalci tare da daina yin duk wani abu da zai iya bata sunan masarautar.
Masarautar ta kuma gargaɗe shi da ya ci gaba da biyayya ga Hakiminsa da sauran masu riƙe da sarauta domin samun shugabanci nagari.
Idan dai za a iya tunawa, a kwanakin baya ne majalisar masarautar Ƙaraye ta sanar da dakatar da Dagaci Ƙauyen Madobawa saboda rashin gudanar da aikinsa yadda ya kamata.
Hakan na cikin sanarwar da jami’in hulɗa da jama’a na masarautar Haruna Gunduwawa ya aikowa Freedom Rediyo.
You must be logged in to post a comment Login