Labarai
Masarautar Kano ta tuɓe Rawani Mai Unguwar Ƴan Doya

Mai martaba San Kano Khalifa Muhammadu Sunusi ll, ya sauke Mai unguwar Ƴan Doya da ke yankin karamar hukumar birni Malam Murtala Hussaini Ƴan Doya daga kan mukaminsa sa bisa samun sa da laifuka da dama, tare da laifuka guda biyu na kin amsa umarnin kiran sarki a lokuta daban-daban da kuma rashin zaman sa a cikin talakawansa.
Mai martaba sarkin ta bakin babban Dan majalisar, matawallen Kano Alhaji Alhaji Aliyu Ibrahim Ahmad, ya bada umarnin sauke Mai unguwar daga kan mukaminsa na Mai unguwa.
Masarautar Kano ta ce, ba zata laminci duk wani rashin gaskiya da cin amana daga kowanne mai rike da sarauta gargajiya ba.
Don haka masarautar ta hori sauran masu rike da masarautu dasu guje rashin gaskiya da neman abun hannun talakawansu.
You must be logged in to post a comment Login