Labarai
Masari tare da DFID sun raba kudade ga wasu dalibai a Katsina
Gwamnatin jihar Katsina tare da tallafin hukumar raya kasashe ta Birtaniya DFID, sun raba kudi naira miliyan 188 ga wasu dalibai mata guda dubu uku da dari bakwa da talatin da biyar, a matsayin tallafin karatu.
Mai taimaka wa gwamnan na Katsina kan harkokin ci gaban ilimin mata Hajiya Amina Lawal Dauda ce ta bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da ta a jiya Alhamis.
Ta ce makasudin tallafa wa daliban shi ne a matsayin su na wadanda suka fito daga karkara domin su samu damar shiga kwalejin ilimi ta Isah Kaita, domin yin karatun NCE.
Haka kuma ta kara da cewa, bayan kammala karatun na su na NCE, za su koma yankunanasu domin koyar da dalibai.
Hajiya Amina Lawal Dauda ta kara da cewa daliban sun fito ne daga kananan hukumomin jihar 34, kuma kowace daliba za ta karbi tallafin Naira dubu hamsin a duk shekara.
You must be logged in to post a comment Login