Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Masari ya karrama matasan da suka kashe dan garkuwa da mutane

Published

on

Gwamantin jihar Katsina da rundunar ‘yan sandan jihar sun karrama wasu matasa da suka yi nasarar kashe daya daga cikin wadanda suka yi garkuwa da su a jihar ta Katsina.

An Karrama matasan uku ne da suka hadar da maza biyu da mace daya biyo bayan tsira da suka yi daga hannun masu garkuwa da mutanen tare da kwace bingida kirar AK-47 da sauran kayan ta’addanci da suke amfani da shi kuma suka mika ga rundunar ‘yan sanda.

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Katsina Sunusi Buba ne ya karramawa matasan a madadin gwamnatin jihar a jiya Talata.

Sunusi Buba ya kuma ce, tun da fari wasu mutane biyu sun yi garkuwa da yaran ne wanda daga bisani suka samu kwarin gwiwar kai musu hari har kuma suka samu nasara.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!