Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Maso abinka: An sace Tirela a Makarfi

Published

on

Rahotanni daga garin Maƙarfi na jihar Kaduna na cewa wani da ba a kai ga gano waye ba, ya yi awon gaba da wata motar Tirela da yammacin jiya Lahadi.

Lamarin ya faru ne a yayin da direban tirelar Nura Ali da abokan aikinsa biyu Surajo Ibrahim da Bashari Musa suka tsaya a Maƙarfin domin cin abinci, sai suka ɗauki wani fasinja da ake zargi da basu alewa daga nan kuma hankalinsu ya gushe.

Wata majiya ta shaida wa Freedom Radio cewa al’umma ne suka garzaya da waɗanda lamarin ya shafa zuwa ofishin ƴan sanda na Kwanar Ɗangora bayan da suka farfaɗo inda suka bada wannan bayani.

Koda muka tuntuɓi mai magana da yawun ƴan sandan Kano DSP. Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce, sun aika da waɗanda lamarin ya shafa zuwa Kaduna kasancewar lamarin ya faru ne a yankin jihar Kadunan.

Kuma mun yi ƙoƙarin jin ta bakin jami’in hulɗa da jama’a na ƴan sandan jihar Kaduna ASP. Muhammad Jalige sai dai kawo wannan lokaci ba mu samu ji daga gareshi ba.

Labarai masu alaka:

‘Yan bindiga sun sace hakimi a Zamfara

An sace kofin Afrika da kasar Masar ta dauka

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!