Labarai
Masu aikin ceto na ci gaba da neman jirgin ruwan sojin Indonesiya da ya yi batan dabo a teku tun a ranar laraba
Masu aikin ceto na ci gaba da neman jirgin ruwan sojin kasar Indonesiya da ya yi batan dabo a ranar larabar da ta gaba.
Rahotanni sun ce jirgin da ke dauke da mutane hamsin da uku ya yi batan dabo ne a wajen shakwata da ke gabar ruwa Bali a kasar ta Indonesia.
Tuni dai jiragen yakin Amurka dana Australia suka shiga cikin tawagar masu farautar jirgin da ya yi batan dabo.
Mai magana da yawun rundunar sojin ruwan kasar ta Indonesia, Julius Widjojono ya shaidawa manema labarai cewa, a yau asabar ne iskar da aka tanadar ma jirgin na kwanaki uku zai kare lamarin da ke nuna cewa, wadanda suke cikin jirgin ka iya mutuwa idan suka wuce yau ba a ceto su ba.
You must be logged in to post a comment Login