Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Masu bada bayanan sirri ga masu garkuwa da mutane sun shiga hannu

Published

on

Rundunar ‘yan sandan jihar Niger tayi nasarar kama wasu mutane biyu da ake zargin suna taimakawa masu yin garkuwa da mutane da bayanan sirri a jihar.

Babban kwamandan yankin na Suleja CSP Sani Badarawa ne ya tabbatar da hakan.

Ya ce, mutanen biyu an kama su ne a unguwar Juma, yayin da rundunar yaki da masu fashi da makami ke gudanar da ran-gadi a yankin.

Shaidun gani da ido a yankin sun bayyana cewa daya daga ciki mai suna Abubakar an kama shi ne bayan ya ajiye abin hawan sa.

CSP Sani Badarawa ya ce, tuni suka aike da wadanda ake zargi zuwa shalwakatar binciken kwakwaf da ke Minna don fadada bincike.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!