Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Addini

KADIRIYYA – Ayi doka da zata ja layi ga masu wakokin batanci

Published

on

Shugaban darikar kadiriyya na Afrika Sheikh Kariballah Nasiru Kabara, ya bukaci gwamnatoci a matakai daban daban da su samar da dokoki masu tsauri da zasu rika hukunta masu batanci kan janibin Annabi Muhammad (S.A.W).

Sheikh Karibullah na bayyana hakan ne a wata tattaunawa da yayi da manema labarai a nan Kano.

Shehin malamin ya bayyana cewa, ya yaba da matakin hukuncin kisa ta hanyar rataya da gwamnatin jihar Kano da majalisar dokokin jihar har ma da kotuna suka dauka kan wani mawaki da yayi kalaman batanci kan janibin Annabi a baya baya nan.

Sheikh Kariballah ya kara da cewa, wannan hukunci na kotu yayi dai-dai da hukunce hukuncen da addinin musulunci ya tsara.

Wakilin mu Muhammad Harisu Kofar Nassarawa ya rawaito cewa, a yayin tattaunawar sheikh Kariballah Nasir Kabara ya jaddada cewa, irin wadannan halaye da dabi’u da mutane suke aikatawa shi ke janyo rashin zaman lafiya da talauci har ma da fushin ubangiji.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!