Coronavirus
Masu Corona a Najeriya sun kai 4,399
NCDC ta ce an gano karin mutane 248 da suka kamu da cutar Covid-19 a ranar Lahadi.
Wanda yakai adadin wadanda aka gano suna dauke da cutar a kasarnan zuwa 4,399.
Mutane 778 daga ciki sun warke an sallamesu.
Sai kuma mutum 143 da suka rasa ransu sanadiyyar cutar ta Covid-19.
A alkaluman yau dai jihar Legas ce kan gaba da mutane 81, sai Jigawa mai mutane 35, sannan jihar Borno mai mutane 26, Kano itama ta samu karin mutane 26.
Mutane 20 a jihar Bauchi, birnin tarayya Abuja na da 13, mutum 12 a jihar Edo sai 10 a Sokoto, mutum 7 a Zamfara, Kwara 4 Kebbi ma 4.
Gombe 2, jihar Taraba ma 2, Ogun 2, Ekiti 2, Osun 1 Bayelsa 1.
You must be logged in to post a comment Login