Coronavirus
Mutane 50 sun warke daga Corona a Kano
Hukumomi a Kano sun ce izuwa yanzu mutane 50 aka sallama bayan sun warke daga cutar Covid-19 a jihar.
Gwamnatin Kano tace a ranar Lahadinnan an gano karin mutane 26 dake dauke da cutar Covid-19 a jihar, wanda hakan ya kai adadin wadanda aka gano sun kamu da cutar a Kano zuwa 602.
Ma’aikatar lafiya ta Kano ta wallafa a shafinta na Twitter cewa an samu karin mutane 5 da suka rasu sanadiyyar cutar, yanzu haka mutane 26 ne suka rasu sanadiyyar cutar Covid-19 a Kano.
#COVID19KN Update as at 11:47pm 10th May 2020
*️⃣ 26 new cases of #COVID19Kano cases confirmed.
*️⃣ Total confirmed cases in @KanostateNg are now 602.
*️⃣ 18 additional #COVID19Kano patients were discharged.
*️⃣ 5 #COVID19Kano deaths were recorded.#MaskUpKano #PrayForKano pic.twitter.com/8qklC4NZx6— Kano State Ministry of Health (@KNSMOH) May 10, 2020
Mutane 526 na cigaba da karbar kulawa daga jami’an lafiya a cibiyoyin killace masu dauke da cutar dake Kano.
Karin labarai:
Wadanda Corona ta hallaka a Kano sun zarce na Abuja
Lock Down: Wani Dan sanda ya koma taya matarsa aikin gida a Kano
You must be logged in to post a comment Login