Labaran Kano
Masu dauke da cuta mai karya garkuwa na fuskantar tsangwama- Nuhu Tela
Mutane masu dauke da cuta mai karya garkuwa sun koka kan yadda sauran al’umma ke nuna tsangwama, a matsayin babban kalubalen da suke fuskanta.
Shugaban masu fama da lalurar cuta mai karya garkuwa Nuhu Tela Gaya ne ya bayyana haka a yayin wani taran bikin ranar ta shekarar 2019 wanda kungiyar CSADI ta shirya don taimakawa masu dauke da cutar garkuwa.
Kungiyar lafiya ta duniya ce dai ta kirkiri wannan rana domin yaki da cuta mai karya garkuwa, da kuma cututtuka da ke da alaka da ita.
Nuha Tela ya ce da dama daga cikin mutane masu dauke da cuta mai karya garkuwa na kunyar nuna kansu sakamakon tsangwama da suke fuskanta tsakanin mutane.
Ya kara da cewa duk da cewar maganin da ke bunkasa garkuwar masu dauke da cutar kyauta ce, amma da yawa daga cikinsu ba su da karfin da zasu yi wasu gwaje-gwajen domin tabbatar da cewar garkuwar jikinsu bai yi kasa ba.
Inda ya ke cewa “wadannan gwaje-gwajen na da maukar muhimmanci, inda suke gwaji na koda, da hanta da sauran gwaje-gwaje da ke taimaka musu.
Daraktar CSADI hajiya Zainab Ahmad Sulaiman ta ce shekaru 20 da suka wuce masu dauke da cutar basa iya nuna kansu saboda tsoron tsangwama da kyara.
Ta ce a yanzu al’umma sun fahimci cewar cuta mai karya garkuwa kamar kowacce irin cuta ce da kowanne dan Adam ba zai so a ce wani nasa na da ita ba.
Ta ce kuma ce masu dauke da cutar na bukatar cin abinci, a yayin da suka sha magungunansu, ammam masu dauke da cutar sickle ko me za su yi cutar tana nan tana kuma motsawa a wasu lokuta ko da an sha magani.