Kiwon Lafiya
Masu sanya idanun kasashen commenwealth sun yaba da hukumar INEC
Masu sanya idanu na kungiyar kasashe rainon Ingila ta commonwealth sun yaba da yadda hukumar zabe ta kasa INEC ta gudanar da zabukan shugaban kasa da na ‘yan majalisun dokokin tarayya a kasar nan.
A cewar kungiyar duk da cewa an fafata sosai a zabukan amma ya bai wa al’ummar Najeriya damar bayyana ra’ayoyinsu da kuma zaben wadanda suke so ba tare da tsangwama ba.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa na wucin gadi da kungiyar ta fitar mai dauke da sa hannun jagoran tawagar kungiyar tsohon shugaban kasar Tanzania Dr. Jakaya Kikwete.
Sanarwar da kungiyar ta Commonwealth ta fitar ta kuma ce zabukan da aka gudanar a ranar Asabar ya nuna karara cewa ‘yan Najeriya suna da hakuri da juriya da kuma biyayya ga tsarin dimukuradiya.
Commonwealth a cewar sanarwar, ta yabawa kokarin jami’an tsaro musamman ‘yan sanda sakamakon namijin kokarin da su ka yi wajen ba da tsaro ga cibiyoyin kada kuri’a.
Sai dai kungiyar ta Commonwealth ta bukaci gwamnatin tarayya da ta yi iya kokarinta wajen ganin cewa an hukunta wadanda suka tada hatsaniya yayin zaben.