Labarai
Mata a karamar hukumar Warawa sun karbi tagomashi
Sama da mata dari biyu Gwamnatin tarayya ta baiwa jarin Naira dubu goma goma a karamar hukumar Warawa domin su dogara da kansu.
Guda na Hukumar Samar da ayyukanyi ta kasa National Directorate of Employment NDE Alhaji Sanusi Yakasai ne ya bayyana hakan yau lokacin bikin rabon jari ga mata ‘yan Asalin karamar hukumar Warawa dari biyu.
A cewar sa tun daga lokacin da Shugaban kasa Buhari ya hau kan mulki yayi alkawarin cigaba da yaki da Talauci domin bunkasa tattalin arzikin al’ummar kasar nan.
Alhaji Sanusi Musa ya kuma yi kira ga matan da suka ci gajiyar samun rabon jarin da su rike jarin hannu biyu- biyu tare da cigaba da gudanar da sana’oin su cikin taka tsan-tsan domin bunkasa jarin na su.
Wakilin mu Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Tukuntawa ya ruwaito cewa cikin wadanda da suka halarci taron akwai Dagacin Garin Dau Alhaji Musa Adamu Musa da Babban Limamin garin Dau da sauran al’ummar Karamar hukumar ta Warawa.