Labarai
Mata basu fiya karbar rashawa ba -Muhuyi Magaji Rimin Gado
Gwamnatin jihar kano ta yi kira ga al’umma a ko wane mataki da su tashi tsaye domin yaki da cin hanci da rashawa ganin yadda matsalar ke kassara tattalin arzikin kasar nan.
Kwamishiyar mata ta jihar Kano Malama Zahra’u Umar ce ta yi wannan kiran ya yin wani taron bita da ma’aikatar kula da harkokin mata da hukumar karbar korafe korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar kano suka shirya don tattauna matsalolin dake addabar mata.
Malama Zahra’u ta kara da cewa mata suna da rawar da zasu taka wajen dakile ayyukan cin hanci da rashawa ta bangaren janyo hankalin mazajensu da su guji karbar na goro.
A nasa jawabin shugaban hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar kano Muhuyi Magaji Rimin Gado ya ce mata basu faya karbar cin hanci ba.
Wakilin mu Shamsu Dau Abdullahi ya ruwaito cewa mata da dama ne suka hallarci taron na wayar da kan mata akan cin hanci da rashawa.
You must be logged in to post a comment Login