Labarai
Mata sun yi zanga-zanga a kano Kan ce-ce kucen kotun Ɗaukaka Ƙara
Yayin da ƙungiyoyin Mata ke tada murya kan cece-kucen Kotun Daukaka Kara Kimanin mata sama da dubu daya ne suka gudanar da zanga-zanga a titunan Kano domin nuna damuwarsu kan batun.
Matan dauke da alluna da kwalaye suna rera wakokin goyon bayan gwamnan jihar Abba Yusuf sun tunkari Shalkwatar Ƴan sandan jihar inda suka mika takarda dauke da korafe-korafensu kan sakamakon hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke
Wannan shi ne karo na farko a tarihin Kano da mata suka fito kan tituna suna neman a yi wa dimokradiyya adalci tare da kare wa’adin zaben gwamna na ranar 18 ga Maris
Daya daga cikin masu zanga-zangar lumana Hajiya Rabi Hotoro ta ce suna kan tituna domin nuna damuwarsu kan abin da ya faru a kotun ɗaukaka kara
“Mun fito ne a yau saboda mun yi imani da dimokuradiyya da ƴancin kai na bangaren shari’a, muna son yin kira ga masu ruwa da tsaki da su yi abin da ya kamata tare da barin ra’ayin jama’ar Kano ya tabbata
” Kano ta fada cikin tashin hankali na siyasa biyo bayan cece-kucen da aka samu daga shari’ar daukaka kara inda hukunci na magana da rubuce-rubuce ya banbanta
You must be logged in to post a comment Login