Labaran Kano
Mata sun kokawa hukumar Hisbah kan cin zarafin mazaje
A yayin da Majalisar Dinkin duniya ta ware Ranar 25 ga watan Nuwamba a matsayin ranar yaki da cin zarafin mata ta Duniya,dubban mata a fadin Duniya sun koka kan yadda suke fuskantar cin zarafi daga mazajensu,ko daga dangin mazajen nasu,ko kuma masu alaka da su ta kusa ko ta nesa.
Anan Najeriya ma,mata kan fuskanci kuntatawa kala-kala daga mazajensu,wanda hakan ke jefa rayuwarsu cikin mummunan yanayi .
Wata mata da muka zanta da ita ta bayyana cewar shekara ashirin suka kwashe da mijinta suna zaman aure,amma duka da cin zarafi da rashin abinci sune suka mamaye rayuwarsu ta aure.
Tace bata tsinci komai a zamantakewarsu ba face cin zarafi.
‘’Saboda dukan da yake mana,sama da shekara ashirin da biyar muke tare da shi,amma daga abu kalilan sai ya dinga wulaqanta ka, a gaban ‘’yayanka zai zauna yana dukanka,kuma idan ya nemeka, ba lafiya ce dashi ba haka zai riqa zirmuka hannu a wuyana yana shakeni”
Harabar rundunar Hizba dake nan Kano cike take da mata masu korafi akan cin zarafi da mazajensu ke yi musu.
Ziyarar da Freedom Radio ta kai ofishin hukumar na zanta da wata mata wadda ta kai korafi kan yadda mijinta yake yawan dukanta
Matan sun shaidawa hukumar Hizba cewa akwai cin zarafi da ya hada da duka har ta kai su ga yin bari