Kiwon Lafiya
Mataimakin shugaban kasa ya gargadi sabbabin mambobin hukumomin kasa kaucewa cin hanci
Mataimakin shugaban kasa, Ferfesa Yemi Osinbajo ya gargadi sabbin mambobin hukumomin kasar kaucewa cin hanci da rashawa a yayin gudanar da ayyukan su
Osinbanjo ya bayyana hakan ne, a ta bakin Sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha, lokacin da yake kaddamar da mambobin zuwa hukumomin da za su aikin su.
Osinbajo ya kuma bukaci mambobin su mayar da hankalan su, don inganta tattalin arzikin kasar nan.
A nasa bangaren, wanda ya yi jawabi a madadin sauran mambobin hukumomin, shugaban cibiyar nazarin harkokin mulkin kasar nan, Mista Ignatius Longian, ce wa ya yi, za su duk mai yiyuwa don ganin sun aiwatar da abun zai daukaka kasar nan a fadin duniya.
Sauran hukumomin sun hada da, hukumar kula da iyakokin kasar nan da kuma hukumar lura da al’ummar da ke zaune a iyaykokin kasar.